Polly po-cket
Android – Tambayoyi 7 da mai amfani da Wayar Android ya kamata ya san amsarsu



Android wacce ake furta ta da Hausa anduroyid manhaja (OS) ce da kamfanin Google Media Inc da ke kasar Amurka ya mallaki lasisinsa wanda shi wannan manhajar ake amfani da ita a kan wayoyin hannu da kuma ƙananan kwamfutocin hannu da ake kira da Table PC. Su irin wannan wayoyi na Android ba kamar sauran waya ba ce kasancewar ita tsarin riƙe ta da tsarin amfani da ita ba a ko’ina ake yi ba. Shi ya sa na ga ya dace in yi mana bayanai a kan waɗansu tambayoyi guda bakwai da ya kamata mai amfani da waɗannan wayoyi ya sani kuma ya san yadda zai amfani da ita. 1) Dole ne sai na yi amfani da Google Accout kafin in iya amfani da Android? Haka yake! Dole duk wanda ya sayi waya ko kuma tablet ya zama yana da account tare da kamfanin google kafin ya yi amfani da ita. Amma wannan ba yakebance cewa akwai wani ɓangare na google accout wanda ya zama wajibi ne a ce shi ne mutum zai yi amfani da shi ba. Abin da ake so kawai ka yi rajista da kamfanin ta wurin mallakar ɗaya daga cikin abubuwan da suke gabatarwa na ayyukansu, kamar gmail da makamantansu. Kodayake google yana ba mutum damar kara wani imel wanda ba google ba, sai dai duk lokacin da mutum yake son ya shiga ya ƙara wa wayar tashi ko tablet dinshi kuzari ko kuma ya kara mata wani application, to dole sai in yana da account tare da google. Kuma akwai waɗansu abubuwa masu matukar amfani ga mai amfani da wayar android ko tablet wanda idan mutum ba ya amfani da account na google ba ne, to ba zai same su ba. 2) Wace hanya ce ta fi kyau wacce zan bi in kwashe duk sunayen da suke cikin wayata? Akwai hanyoyin da mutum zai iya bi domin ya ga ya kwafe tsofaffin lambobin cikin wayarsa zuwa wayarsa ta android. Ɗaya daga cikin hanyar shi ne mutum zai iya buɗe google sai ya shiga dakin aikawa da sakon imel wanda ake kira da gmail, to sai ya rubuce dukkanin sunayen da ke wayarsa daga nan lambobin da kansu za su dawo cikin wayarsa ko kuma tablet pc ɗin shi. Ko kuma ka yi amfani da tsohuwar hanya na kwafe lambobinka a cikin SIM ɗinka sannan ka saka shi cikin wayar android ko tablet sannan ka kwafe shi cikin ta. 3) Mene ne dalilin da ya sa wayoyin android ba sa kama da juna? Kamfanin google su suka kirkiri manhajan Android amma kuma sai suka bai wa kamfanonin da suke yin waya damar su yi amfani da wannan manhajar a cikin wayoyinsu. Saboda haka shi ya sa kake ganin fuskokin da kuma kamanninsu ya banbanta. Kamfanonin da suke da wannan lasisi sun haɗa da kamfanin Samsung da kuma kamfanin HTC, wanda waɗannan kamfanonin kowannensu, kera waya da kuma kayan Kwamfuta yake yi. Saboda haka kowane ɗaya daga cikinsu yana da damar ya yi irin kalar waya ko kuma tablet da yake ganin za ta amsu a hannun abokanen cinikinsa. 4) To yaya za a yi in samu android wacce ba ta waɗancan kamfanonin ba? Idan baka son ɗaya daga cikin wayoyin da kamfanin HTC ko Samsung suke yi, to ai kamfanin google yana da tashi wayar mai suna NEXUS. Wanda aka fi sani da Nexus 7 Tablet da kuma Galaxy Nexus Phone. Waɗannan guda biyu da manhajar da kuma karafan da suke jikinsu duk mallakar kamfanin google ne. Sannan kuma su waɗannan wayoyi ko da wane lokaci kamfanin google yana ƙoƙarin inganta su ta wajen manhajin da suke amfani da su, kasancewar suna samun komai kai tsaye daga wurin google. Su kuwa sauran wayoyi kamar na HTC da Samsung waɗanda suke amfani da manhajar android sukan ɗauko wani lokaci mai tsawo kafin a waiwayi manhajar tasu, domin abu ne mai yawa da kuma faɗi da kuma abubuwan da waɗancan kamfanonin suke yi yana musu yawa.5) Mene ne banbanci tsakanin Home Screen da kuma App Drawer? ShiApp Drawershi ne wurin da za ka samu dukkanin application da ka ɗaura wa android, an kira wurin da Drawer kamar yadda malam Bahaushe ya sani da matsayin rumbu kasancewar nan ne ake samun abubuwan da aka ajiye a ciki. Saboda haka Adroid suna da fallaye guda bakwai da suka baka damar ka fito da dukkanin application da kake yawan aiki da su, domin samun sauƙi. To, waɗannan application da ka saka a kan wannan falle shi ake kira daHome Screen. Su kuma application da baka son ganinsu a wannan fallen su kuma suna cikinApp Drawer. 6) Mene ne Widgets? Widget kamar yadda ake furta su da Hauwa “wijet” suna da amfani matuka domin su ana amfani da su wajen bayar da waɗan su bayanai da kuma tattalin wutar batirin android. Su kamar hotuna ne na waɗansu application da ka saka a cikin Home Screen ɗin ka wanda za su riƙa faɗa maka abubuwan da yake gudana ƙarƙashin waɗannan application da ka saka su a cikin wijet ɗin. Misali wanda ya ɗauko application na facebook ko twitter ko na gmail ya saka a cikin wijet to duk sakon da ya shigo, ɗaya daga cikin waɗannan application ɗin zai ga matashiya kai tsaye wanda ba sai ya buɗe shi application karan kansa ba. 7) Ina da abubuwan saurare a itunes zan iya sauraronsu a android dina? Akwai wani software da ake kira da doubleTwist yana aiki kamar yadda ka san Itunes yake yi. Saboda haka idan ka ɗaura shi zai baka damar saukar da duk abin da kake da su a Itunes zuwa Android ɗinka.